Dara Na Cin Gida A Hare-Haren Kunar Bakin Wake A Gombe

  • Ibrahim Garba

Wasu bama-baman da aka bankado a Gombe a makon jiya

A baya bayan nan, yinkurin kai hare-hare a Gombe ya kan ci tura ta yadda wani zubin ma dara ce kan ci gida. Ma'ana, 'yan kunar bakin wake sun yi ta tarwatsa kansu tun kafin su isa inda su ka nufa

A daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan sabuwar shekara ta 2015, su kuma ‘yan kunar bakin wake sai tsananta kai hare-hare su ke yi – musamman ma a garin Gombe. To saidai dara ce ta ci gida a jerin hare-haren da su ka yi ta yinkurin kaiwa.

Wakilinmu a shiyyar Bauchi Abdulwahab Muhammad ya aiko da rahoto kan yadda kaikayi ya koma kam mashekiya a jiya Laraba da kuma safiyar yau Alhamis, inda bama-bamai su ka yi ta tashi da masu niyyar kai harin kunar bakin wake tun kafin su kai wurin da su ke so. Don haka su kadai bama-baman su ka hallakar.

Wakilin na mu ya ruwaito kakakin ‘yan sandan jihar Gombe DPS Faji Attajiri na bayyana abin da ya faru da cewa, maharin na yau bisa babur yak e. Ya ce maharin ya kasa kaiwa ga wurin da ya yi niyyar kai wa ne saboda ingantattun matakan tsaron da aka dauka. Y ace bam din ya tarwatsa maharin shi kadai, in banda wadanda ke kusa da wurin, wadanda su ka dan samu raunuka. Ya maharin namiji ne kuma ya na da wani irin zanen da bai yi kama da na ‘yan Nijeriya ba. To saidai ya ce ba zai sake bayanin harin jiya ba. Haka zalika, wani ganau ya tabbatar da cewa daga kugun maharin zuwa kasa duk ya yi rugu-rugu ta yadfda har hanjinsa ke waje.

Your browser doesn’t support HTML5

Hare-haren Bama-bamai A Gombe