DARDUMAR VOA: Allah Ya Yi Wa Jaruma Daso Saratu Gidado Rasuwa

Your browser doesn’t support HTML5

A ranar Talata, 9 ga watan Afrilu ne masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood a Najeriya ta girgiza da babban rashin daya daga cikin jarumanta. Saratu Gidado da aka fi sani da Daso ta rasu ne a Kano bayan ta yi sahur na ranar karshe ta azumin watan Ramadan ta koma barci.