Dokar Jihar Ekiti Ba Zata Kawar da Rikici Ba - Makiyaya

Kiwon shanu

Wasu kungiyoyin makiyaya na Nigeria sunce sababbin dokokin da gwamnatin daya daga cikin jihohin kasar ta kafa a kwannakin nan ba zasu yi maganin rigingimmun dake yawan barkewa tsakaninsu da manoma ba, abinda ya sha janyo asaran rayukkan mutane da yawa a kasar.

A ranar Litinin da ta gabata ne gwamnan jihar Ekiti dake kudu-maso-yammacin Nigeria, Peter Ayodele Fayose, ya rattaba hannu akan wata dokar da ta takaita kiyon dabbobi akan wasu kebatattun wurare na hukuma, kuma kiyon da rana kawai aka yarda a yi shi, sannan kuma ta haramta wa makiyaya daukar makamai.

Wani kakakin gwamantin ta Ekiti yace fitowa da wannan dokar ta biyo ne bayan barkewar fadace-fadacen da suka faru ne a kwanan nan a tsakanin manoma da makiyaya.