Dole A Ba Kananan Hukumomi Kudaden Su Kai Tsaye

Shuwagabanin kananan hukumomi a Najeriya, sun yi na’am da tsarin nan da gwamnatin tarayya ta bullo da shi na ba kananan hukumomi kudadensu kai tsaye, wanda suka ce zai amfani jama’a musamman a karkara.

Tsarin ba kananan hukumomin kudadensu kai tsaye dai, an yi ne ta yadda kananan hukumomin zasu samu sukunin aiwatar da ayyukan da zai basu dammar samun hanyoyin shigar kudi, biyan haraji da jangali daga al’umma da sarrafa kudaden bisa bukatun da al’umma ke da shi ba tare da tsangwama daga gwamnonin jihohi ba.

Shugaban kungiyar kananan hukumomin jihar Filato, wanda shine shugaban karamar hukumar Mikang, Ezekiel Vuelgap yace har yanzu dokar bata fara aiki ba, kuma yawancin kananan hukumomi basu samu kudi a asusunsu na kai tsaye ba.

Shugaban karamar hukumar Lafia a jihar Nasarawa, Aminu Mu’azu Maifata yace tun can basu da wata matsala wajen rabon kudin kananan hukumomi, sai dai kason da kananan hukumomin ke samu yayi karanci.

Sashe na dari da sittin da biyu na kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda dokar ta tabbatar da cewar dole kudin kananan hukumomi su shiga asusu guda kafin a raba, abinda tsohon shugaban karamar hukumar Fankshin a jihar FPilato, Steven Jings yace sai an gyara kafin kananan hukumomin su sami kudaden su kai tsaye.