DOMIN IYALI: Tattaunawa Kan Fatali Da Kudurorin Ba Mata Kason Guraban Mulkin Najeriya-Kashi Na Daya-Maris, 31, 2022

Alheri Grace Abdu

Burin mata a Najeriya na samun kaso talatin da biyar na guraban siyasa ya gamu da cikas bayan da majalisar dokokin kasar ta yi fatali da kudurin a farkon wannan watan, lamarin ya harzuka mata suka gudanar da zanga zangar lumana a birane da dama na kasar, da kuma lasar takobin ci gaba da tada kayar baya sai hakar su ta cimma ruwa.

Batun da shirin Domin Iyali ya fara haska fitila ke nan a wannan shirin. Bakin da muka gayyata sun hada, tsohuwar Ministar mata Aisha Isma’il, da Barrista Hassana Ayuba Mairiga, da kuma ‘yar gwaggwarmaya Balaraba Abdullahi:

Saurari tattaunawar da Madina Dauda ta jagoranta.

Your browser doesn’t support HTML5

DOMIN IYALI: Tattaunawa Kan Fatali Da Kudurorin Ba Mata Guraban Mulkin Najeriya-Kashi Na Daya-10:00"