DOMIN IYALI:Tattaunawa Kan Zaben Mata A Matsayin Shugabanci Kashi Na Uku -Maris 04, 2021

Alheri Grace Abdu

Idan kuna biye da mu, Shirin Domin Iyali yana nazarin ci gaban da ake samu a kasashen duniya dangane da samun mata a manyan madafun shugabanci. A yau bakin da muka gayyata a shirin sun haska fitila kan kalubale da mata ke fuskanta.

Domin nazarin yadda mata a kasashen nahiyar Afrika za su dora a wannan ci gaban da ake samu, yau ma muna tare da Shugabar gamayyar kungiyoyin mata a Najeriya Madam Gloria Laraba Shoda, da hajiya Balaraba Mohammed shugabar kungiyar Mata Fulani ta babban birnin Tarayya Abuja, da kuma Hajiya Sa’adatu Ahmed Bustani mazauniyar birnin tarayya Abuja.

Saurari tattaunawar da Madina Dauda ta jagoranta:

Your browser doesn’t support HTML5

DOMIN IYALI:Tattaunawa Kan Zaben Mata A Matsayin Shugabanci- Kashi Na Uku 10:00"