Dubban Mutane Na Cikin Mawuyacin Hali a Monguno - MSF

Muna, daya daga cikin sansanoni da 'yan gudun hijira ke samun mafaka a birnin Maiduguri da ke arewacin Najeriya

“Mutanen da suka tserewa yankin Monguno a kwanan nan, sun fice daga gidajensu inda suka bar komai a baya, yanzu suna kwana ne a kan tituna.” Inji wani jami’in kungiyar ta MSF Musa Baba.

Akalla mutum 30,000 ne ke fuskantar matsananci yanayi na bukatar mafaka da sauran bukatun yau da kullum na rayuwa a garin Monguno da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

Mutanen sun tsere ne daga gidajensu, sanadiyar artabun da dakarun gwamnati ke yi da mayakan masu dauke da makamai, kungiyar likitoci ta kasa da kasa ta MSF ta fada a jiya Talata.

An shiga matsanancin hali na rayuwa a jihar ta Borno cikin shekaru goma da aka kwashe ana rikici da mayakan Boko Haram.

Tun daga watan Disambar bara, an ci gaba da samun karuwar tashe-tashen hankula, lamarin da ya tilastawa dubban mutane tserewa zuwa garuruwan da ke hannun dakarun gwamnati a cewar wata sanarwa da kungiyar ta MSF ta fitar dauke da sa hannun jami’in yada labaranta, Tim Shenk.

“Mutanen da suka tserewa yankin Monguno a kwanan nan, sun fice daga gidajensu inda suka bar komai a baya, yanzu suna kwana ne a kan tituna.” Inji wani jami’in kungiyar ta MSF, Musa Baba.

Kungaiyar likitocin, ta yi kiran samar da wani tsari mai inganci a tsakanin bangaren gwamnatin Najeriya da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyo masu zaman kansu, domin ganin an tunkari matsalolin da ‘yan gudun hijirar ke fuskanta.