Dubban 'Yan Gudun Hijiran Najeriya Sun Tsere Zuwa Nijar

Wasu 'yan gudun hijirar Najeriya

Sama da ‘yan gudun hijira dubu 20 da ke tserewa hare-haren ‘yan bindiga a jihar Sokoton Najeriya ne suka fantsama zuwa cikin jihar Maradi da ke Jamhuriyar Nijar domin neman mafaka, inji hukumomin Nijar.

Yayin wata ganawa da manema labarai a lokacin da ya ziyarci 'yan gudun hijiran, gwamnan jihar Maradi, Zakari Ummaru, ya nuna bukatar a hada kai tsakanin Nijar da Najeriya domin a kawo karshen wannan matsala ta tsaro wacce ke ta da hankulan jama'ar yankunan biyu.

“Mutum fiye da 20 suke nan, muna tattalinsu, daga kasar Sokoto suka fito. Gamuwa muka yi da wannan jama’a ba su san ma inda za su ba” Inji gwamnan Ummaru.

Kalaman gwamnan na zuwa ne bayan wani hari da aka kai a garin Shirgi da ke yankin Madarumfa a jihar ta Maradi, inda har mutum biyar suka mutu.

“Ba mu san dalilin harin nan ba, Najeriya ‘yan uwanmu ne na jini zumuntarmu da su ba za ta katse ba, mu gama karfinmu da su mu yi maganin wannan abu, mu a shirye muke.”

A karshen makon da ya gabata ne wasu mahara suka far wa yankin karamar hukumar Goronyo da ke jihar Sokoto suka kashe mutum 37.

Wata sanarwa da fadar shugaban Najeriya ta fitar a jiya Asabar dauke da sa hannu mai ba shugaba Muhammadu Buhari shawara kan harkar yada labarai Garba Shehu, ta mika sakon jaje ga al’umar jihar ta Sokoto bisa wannan hari.

Sanarwar ta kara da cewa, hukumomin na daukan dukkan matakan da suka dace domin ganin an tabbatar da tsaron lafiyar jama'a da dukiyoyinsu.

Saurari cikakken rahoton Tamar Abari daga Maradi:

Your browser doesn’t support HTML5

Dubban 'Yan Gudun Hijiran Najeriya Sun Tsere Zuwa Nijar - 2'29"