DUNIYAR AMURKA: Barazanar Kutsen Rasha, Mutuwar Madeleine Albright Da Zabin Ketanji Jackson Brown, Maris 25, 2022

Mahmud Lalo

Shugaba Joe Biden, ya yi gargadin cewa, akwai yiwuwar Rasha ta kai hari kan rumbun adana bayanai a wasu wurare a Amurka ko kuma ta yi amfani da makamai masu guba a Ukraine yayin da mamayar da Rashar ta yi wa kasar ta Ukraine ta doshi wata guda. 

Sannan za ku ji abin da manyan jami’an gwamnatin Amurka ke cewa kan rasuwar tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Madeleine Albright, za kuma mu duba inda aka kwana kan batun kokarin tantance mai shari’a Ketanji Brown Jackon da majalisar Dattawa ke yi don duba cancantarta bayan da Shugaba Biden ya zabeta don zama alkaliya a kotun kolin kasar.

Your browser doesn’t support HTML5

DUNIYAR AMURKA: Barazanar Kutsen Rasha, Madeleine Albright Da Ketanji Jackson Brown - 6'00"