DUNIYAR AMURKA: Matsalar Karancin Masu Ba Da Gudunmawar Jini A Amurka, Janairu 19, 2024

Mahmud Lalo

Zubar dusar kankara da ruwan sama da kuma mummunar guguwa da ake fuskanta a sassan Amurka, na daga cikin dalilan da suka sa jama'a suka kauracewa cibiyoyin ba da gudunmawar jini a Amurka a cewar Red Cross.

Kungiyar ba da agajin ta kasa da kasa Red Cross a nan Amurka ta koka kan yadda ake samun karancin masu ba da gudunmawar jini a kasar inda ta ce rabon da a ga irin wannan karanci tun shekaru 20 da suka gabata.

Your browser doesn’t support HTML5

DUNIYAR AMURKA: Matsalar Karancin Masu Ba Da Gudunmawar Jini A Amurka.mp3