ECOWAS Tana Taron Koli A Ghana

Shugaban Kasar Ghana John Dramani Mahama

Shugabannin kasashe da suke cikin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS suna taron koli a Kasar Ghana.

Kungiyar dai na tattaunawa kan yaki da cutar Ebola dakuma hana cutar yaduwa a kasashen yammacin Afirka dama nahiyar Afirka baki daya. An dai sami halartar shugabanni da yawansu yakai bakwai, dakuma wakilan sauran shugabannin da basu sami halartaba. Zaman na yau dai an maida hankali kan cutar Ebola, an baiwa kasahen ukun da wannan annoba ta addaba dama suka kawo jawabansu, a zaman gobe Juma’a kuma za’a tattauna kan abinda ke faruwa a Burkina Faso.

Kasashen da annobar cutar da addaba Laberiya, Saliyo da Guinea, kasashen dai sunyi bayyana matakan da suke dauka a kasashen domin ganin sun dakile wannan annoba, dakuma neman karin taimakon da suke bukata don cimma burin ganin an kawar da cutar baki daya.

Your browser doesn’t support HTML5

ECOWAS Tana Taron Koli A Ghana - 4'22"