ECOWAS: Taro Fadakar da Jama'a Illar Halalta Kudaden Haram

Wasu shugabannin kasashen yammacin Afirka

Taron na kungiyoyin gwamnatocin kasashen yammacin Afirka zai fadakar da jama'a akan yaki da kudaden haram da aka samu ta hanyar sata ko sarafa miyagun kwayoyi.

Bayan fadakar da mahalarta illar dake tattare da halalta kudaden haram da ake samu walau ko ta safaran miyagun kwayoyi da satar dukiyar kasa daga jami'an gwamnatoci da 'yan siyasa.

Taron zai tabo batun anfani da kudaden wajen safaran muggan kwayoyi ko makamai domin ayyuka irin na ta'adanci tsakanin kasa da kasa.

Wannan taron dai ya zo daidai lokacin da kasashe irinsu Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru da Mali ke fuskantar ayyukan ta'adanci. Wakilai daga kasashen yammacin Afirka suke halartar taron.

Mr. Timothy Mailaya wakilin kungiyar GIABA a Najeriya yayi karin haske akan mahimmancin taron. Yakin da suke yi da kudaden haram yana cigaba kuma suna samun nasara saboda wayar da kawunan jama'a..Mutane sun fara ganewa da kudaden haram da kuma illarsu.

Hakin kowane dan kasa ne musamman a Najeriya ya san menen gwamnati ta keyi da dukiyar jama'a. Haka ma za'a san abun da kamfuna keyi da nasu kudaden.

Wani Malam Lawali Tsayyabu shugaban kungiyar farar hula daga Jamhuriyar Nijar ya bayyana irin rawar da kungiyoyin fafaren hula zasu taka a yaki da kudaden haram a tsakanin kasashen yammacin Afirka.

Garahoton Babangida Jibrin da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

ECOWAS: Taron Fadakar da Jama'a Illar Halalta Kudaden Haram