EFCC Ta Kama Tsabar Kudi Naira Miliyan 49

Tambarin EFCC

Samun wasu makudan kudade da yawansu ya kai Naira miliyan 49 a filin tashin jirgin saman Kaduna da hukumar EFCC ta yi, na nuna irin nasarar da ake samu a yaki da cin hanci a Najeriya, a cewar hukumar.

Jami'in hukumar ya ce bayanai ne da suka samu na tsegumi suka nuna akwai kudi da aka boye a buhuna, dalili da ya sa suka garzaya inda suka samu kudin.

Jami'in labarun hukumar EFCC Wison Uwujeren ya yi wa manema labarai karin haske akan lamarin karbe kudin da ake ganin na haramun ne.

Ya ce ana ci gaba da samun nasara akan yadda mutane ke tseguntawa hukumar inda aka boye kudin da aka tara ta hanyar ba ta dace ba.

Ya zuwa yanzu babu wanda ya fito fili ya ce kudadensa ne

Domin jin cikakken bayani kan wannan lamari saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

EFCC Ta Kama Tsabar Kudi Naira Miliyan 49 - 2' 52"