Ethiopia: An Ba Abiy Ahmed Kyautar "Nobel" Ta Zaman Lafiya

Firai Ministan Ethiopia, Abiy Ahmed

An karrama Firai Ministan Ethiopia, Abiy Ahmed da kyautar Nobel ta zaman lafiya a wannan shekara, saboda rawar da ya taka wajen kulla yarjejeniyar zaman lafiya ta 2018 tsakanin kasarsa da Eritrea.

Kasashen biyu sun kwashe shekaru da dama suna rikici akan iyakokinsu.

Yayin da yake karbar kyautar a birnin Oslo a yau Talata, Ahmed ya jaddada burinsa na ganin cewa an tabbatar da zaman lafiya a tsakanin kasashen biyu

“Na yi amannar cewa, ana gab da samar da zaman lafiya tsakanin Ethiopia da Eritrea, na kuma tabbata cewa, akwai bukatar a kawar da bangon da ke tsakanin kasashenmu."

Firai ministan na Ethiopia, ya kuma ce, a madadin bangon za a samar da wata kafa da za ta karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu.

“A maimakon haka, za mu gina wata gada ta kawance, wacce za ta zauna har abada.” Ya kara da cewa.

Abiy ya ce wannan kyauta, ba tashi ce shi kadai ba, har da shugaban Eritrea Isaias Afwerki, “ wanda kyakkyawar niyyarsa ta sa aka samu maslaha kan wannan takaddama da aka kwashe shekara 20 ana yi tsakanin kasashen.”