Farfadowa da Sana'ar Saka a Garin Agayawa Kashin na Biyu

Wasu maza suna saka a Agayawa jihar Katsinan Nigeria

Hukumar samar da ayyukan yi ko NDE a takaice, ita ce ta dauki nauyin farfado da sana'ar saka a garin Agayawa dake jihar Katsina

Malam Abubakar Muhammed daraktan hukumar NDE yace suna bin duk kowane fannin tattalin arziki domin su kirkiro aikin yi dalili ke nan da hukumarsa ta dauki nauyin farfado da sana'ar saka a garin Agayawa.

A hukumance ba'a hana hukumar shiga kowane fanni ba. Sana'ar saka tana ba mutane da dama aikin yi. Akwai batun rini. Akwai batun dinki. Akwai batun kada zabe. Akwai batun talla da dai sauransu. Sabili da haka idan aka farfado da sana'ar saka za'a farfado da wasu ayyuka da dama, mutane kuma zasu samu aikin yi, musamman ga mutanen dake karkara.

Mutanen Agayawa sun iya sana'ar amma kuma tana neman mutuwa. Duk masu yin sana'ar a Agayawa 'yan shekaru saba'in ne zuwa sama. Ke nan idan sun tafi sana'ar zata mutu idan babu wadanda suka soma koya yanzu su gajesu.

Sai hukumar NDE ta tattarosu ta nuna masu cewa bai kamata su bari sana'ar ta mutu ba. Ga matasa basu da aikin yi. Ga sana'a zata bace. To sai hukumar ta tattarosu da matasan suka gina santa tare da sawo masu kayan aiki da duk abubuwan da suke bukata. Kana suka kira matasa suka fada masu gwamnati ta fita hakinsu domin ga abun koyon aikin gadonsu nan.

Ta sabili da haka suka sa matasa suka soma koyar sana'ar domin su huta da zaman kashe wando.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Farfadowa da Sana'ar Saka a Garin Agayawa Kashin na Biyu - 2' 45"