Fashewa Ta Halaka Mutum 10 a China

Wani kamfanin sarrafa karafa a kasar China

Wata fashewa da ta auku a tashar gas a Lardin Henan da ke tsakiyar China, ta halaka akalla mutum 10 kana wasu 19 sun jikkata.

Hukumomin sun ce ba san inda wasu mutane biyar suke ba, bayan wannan fashewa, wacce ta auku a jiya Juma’a a kamfanin gas na Henan Coal Gas Company.

Kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ruwaito cewa, ya zuwa yanzu, an dakatar da duk wasu aikace-aikace a kamfanin.