FIFA ta girmama marigayi Rashidi Yekini shahararren dan wasan kwallon kafan Najeriya

Gianni Infantino, shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA

Jiya Laraba shahararren dan wasan kwallon kafa na Najeriya Rashidi Yekini ya cika shekaru hudu da rasuwa yana da shekaru arba'in da takwas a duniya.

Rashidi Yekini ya rasu ne a ranar hudu ga watan Mayun shekarar 2012 kuma hukumar kwallon kafa ta duniya, wato FIFA, ta girmamashi a shafinta na Internet inda ta bada takaitacen tarihinsa.

Rashidi Yekini dai ya kasance dan wasan kwallon kafan Najeriya daya tilo da ya ci kwallaye har talatin da bakwai a wasanni daban daban da Najeriya ta buga.Kawo yanzu babu wani dan wasan Najeriya da ya kama kafarsa.

Kafin rasuwarsa dan wasan kwallon ya buga wasanni irin na kwararru a kasashen Spain da Greece da Portugal da kuma Switzaland.

Wani mai koyas da 'yan wasan kwallon kafa Ade ya kasance daya daga cikin wadanda suka horas da Rashidi Yekini.Yace mutum ne mai hazaka a wasan kwallo. Yana da hakuri da biyayya. Duk abun da aka sashi ya yi da shafi wasan kwallo baya ki.

'Yan Najeriya sun ji dadin abun da FIFA ta yi masa suna cewa da an samu mutane irinsa da Najeriya ta samu daukaka a wasan kwallo a duniya. Suna fatan zasu yi koyi dashi. An kira gwamnati ta taimakawa iyalansa.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

FIFA ta girmama marigayi Rashidi Yekini shahararren dan kwallon kafan Najeriya - 3' 12"