FIFA Ta Ladabtar Da Kungiyar FC Barcelona - 2/4/2014

Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, ta haramtawa kungiyar FC Barcelona daukar wani sabon dan wasa a kakar kwallo ta shekara mai zuwa, a bayan da aka same ta da laifin keta dokokin hayar ‘yan wasa a yau laraba.

Wannan hukumci mai tsanani da FIFA ta yanke a kan Barcelona, wanda zai shafi lokutan dauka ko hayar ‘yan wasa na daminar bana da kuma watan Janairu mai zuwa, ya biyo bayan binciken shekara guda da aka gudanar kan yadda kungiyar ta dauki ‘yan wasa ‘yan kasa da shekara 18 daga 2009 zuwa 2013.

FIFA ta ce daukar wasu ‘yan wasa 10 da ba a fadi sunayensu ba da Barcelona ta yi, ya saba ma ka’idojin hukumar na kare yaran da ba su balaga ba.

Haka ita ma hukumar kwallon kafa ta kasar Spain an same ta da laifin keta ka’idojin yin rajistar ‘yan wasan da shekarunsu bai kai 18 da haihuwa ba, an kuma yanke mata tarar kimanin dala dubu 565.

Ba a bayar da karin bayani game da wannan lamarin ba, amma kuma a watan Fabrairu, kungiyar Barcelona ta ce hukumar FIFA ta umurce ta da kada ta dauki wasu ‘yan wasa su 6 ‘yan kasa da shekara 18 domin kungiyarta ta matasa. ‘Yan wasan sun hada har da wani yaro dan asalin Najeriya mai suna Bobby Adekanye