Fulani Na Kai Harin Kisan Dauki Dai-dai A Jihar Adamawa

Gwamnan jihar Adamawa Muhammad Jibrilla Bindo

Manoma da ke zaune a kauyukan Luggere- Demberi, Sanbi da Womsara a gundumar Yadim na karamar hukumar Fufore dake jihar Adamawa sun soma kaurar da yara da mata zuwa kauyuka makwabta sakamakon barazanar da harin kisan dauki dai-dai da Fulani makiyaya ke yi a gomnaki da ya yi sanadin kashe manoma hudu makonni uku da suka gabata.

Mazauna yankin sun sorata biyo bayan irin sa da ya faru a Koh watan Junairu da Kodamun a watan Yuli inda rayuka sama da tamanin suka salwanta. Dalili kenan da ya sanya dattawansu kai kokensu ga masarautar Yadim da ofishin ‘yan sanda na yanki domin sanar da su halin zaman dar-dar da ya hana su zuwan gonakinsu.

Hari na baya-bayan nan ya yi sanadi mutuwar wani manomi da wata mata Malama Apolona da yanzu haka ke jinyar raunuka da ta samu daga sara a gonarta.

Apolona da Fulani suka sara a Adamawa

Wakilinmu Muryar Amurka ya tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda na jihar adamawa S.P Othman Abubakar wanda ya ce ba'a sanar da rundunar abkuwar lamarin ba. Yayin da kokarin da ya yi don jin ta bakin masarautar Adamawa ya cutura.

Lokacin da wakilinmu ya ziyarci yankin ya iske dattawan yankin karkashin jagorancin Jauro Sanbi Baba Robert Njidda sun kai koke gaban hakimin Yadim Alhaji Jika Bunu da ofishin ‘yan sanda na yankin. Kawo yanzu babu wanda jami’an tsaro suka kama ana zargi da aikata laifin.

Wannan mataki na dattawan na zuwa ne, a jihar da ke fama da irin rikicin sakanin Fulani da makiyaya da manoma da a wasu lokuta kan kazance har ya kai ga asarar daruruwar rayuka.

Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Fulani Suna Kai Harin Kisan Dauki Daidai A Jihar Adamawa - 3' 11"