Fulanin Nijar Sun Yi Watsi Da Shawarar 'Yan Ta'adda

NIGER: Taron Fulani Makiyaya

Yinkurin 'yan ta'adda na zurma al'ummar Fulanin Janhuriyar Nijar cikin harkar ta'addanci ya ci tura bayan da Fulanin su ka yi banza da zawarcin 'yan ta'addan.

Wasu shuwagabanin kungiyoyin ‘yan ta’addan arewacin Mali sun bukaci al’ummar fulanin kasashen Afirka ta Yamma su ci gaba da jihadi a wannan yanki, sai dai tuni shuwagabannin wata kungiyar makiyayan Jamhuriyar Nijar suka yi watsi da wannan kira da su ke ganinsa a matsayi wani shirme.

A watan videon da aka saka a yanar gizo da yammacin Alhamis din da ta gabata ne shuwagabanin kungiyoyin da suke kiran kannsu na jihadi, wadanda suka hada da tsohon jagoran ‘yan tawayen Mali Iyad Ag Ghali da dan kasar Algerian nan da ke shugabancin reshen Alka'ida a yankin Maghreb Djamel Okacha da ake kira Yahia Abdul Hammam da Amadou Kounfa wani mai wa’azi irin na masu tsatsauran ra’ayin addini suka bukaci al’umar Fulanin kasashen Afirka ta yamma ta ci gaba da jihadi a wannan yanki kiran da kungiyar makiyayan arewacin Tilabery a ta bakin shugabanta Boubakar Diallo ta yi watsi da shi. …

A wannan video Amadou Kounfa ya yi amfani da harshen Fulatanci domin aika sako zuwa ga mutanen da ya kira ‘yan uwansa abin da shuwagabanin makiyaya ke kallonsa tamkar wani salon yaudara.

Ga dai wakilinmu a Yamai Sule Barma da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Al'umar Fulani Kasar Nijar Ta Yi Watsi Da Tayin Kungioyin Ta'a'ddancin Kasar Mali