Gaggauta Komawa Harkokin Yau Da Kullun Zai Janyo Hatsari a Amurka - Fauci

Wani Babban masani akan cututtuka masu yaduwa na Amurka, mai suna Dr. Anthony Fauci, yayi gargadi akan abin da ya kira, "babbar kasadar" yiwuwar dada yaduwar cutar nan mai kisa ta coronavirus, muddun Amurka ta gaggauta sake komawa harkokin yau da kullun.

Ya fadi hakan ne saboda kokarin da Shugaba Donald Trump ke yi na sake bude kamfanoni ran daya ga watan Mayu.

Fauci ya fada wa gidan talabijin na CNN cewa sake farfado da hada hadar kasuwancin Amurka ba zai yiwu nan take ba, yayin da umurnin gwamnati na bayar da tazara tsakanin jama'a don kare kai ke kawo karshe ranar 30 ga watan Mayu.

Yana sa ran “a kalla ta wasu hanyoyin” kasar ka iya koma gudanar da ayyukan yau da kullun a watan gobe, to amma ya ce hakan zai danganta ne ga yanayin ko wane wuri a kasar.