Gaskiya Ta Yi Halinta

Kelly Renee Gissendaner wadda aka sameta da laifin kashe mijinta

Wata da ta kashe mijinta tun shekarar 1997 yanzu wata kotu a jihar Georgia nan Amurka ta sameta da laifin kisan

A jihar Georgia dake kudu maso gabashin Amurka, an zartas da hukuncin kisa kan wata mace, wacce kotu ta sameta da laifin kashe mijinta a shekara 1997, duk da matakan neman dakatar da aiwatar hukuncin da aka tayi, da kuma kiran da Fafa Roma Francis yayi kansa na neman a yi mata afuwa.

Matar mai suna kelly Gissendaner, yar shekaru 47 da haifuwa an kasheta ne ta wajen yi mata allura a wani gidan fursina dake fitar Atlanta babban birnin jihar. Kelly itace mace kadai dake dakon hukuncin kisa a jihar, kuma itace ta farko da jihar ta aiwatar da hukuncin kisa akanta tun 1945, watau shekaru 70 kenan.