Gidauniyar Bill Da Melinda Gates, Da Gidauniyar Dangote Zasu Raba Najeriya Da Cutar Polio Nan Da Karshen 2014

Bill da Melinda Gates

Mr. Bill Gates, shi ya bayarda wannan tabbacin a karshen rangadin kwanaki biyun da ya kai Najeriya don yakar cutar Polio
Gidauniyar Bill da Melinda Gates, tare da hadin kan Gidauniyar Dangote, sun kuduri aniyar kawar da cutar Polio a Najeriya nan da karshen shekara mai zuwa ta 2014.

Mr. Bill Gates, shi ne ya bada wannan tabbacin a Lagos, a karshen rangadin kwanaki biyun da ya kai Najeriya na yaki da cutar Polio.

Mr. Gates, wanda shi ne shugaban kamfanin sarrafa na'urorin Kwamfuta na zamani na Microsoft, yace ya samu nasarar ziyarar da ya kai wasu sassan Najeriya, ya kuma ytaba da kudurin da ya ce ya gani daga gwamnatin Najeriya na kawo karshen cutar Polio a kasar.

Shi kuma Alhaji Aliko Dangote, shugaban jerin kamfanonin Dangote Group, yace 'yan Najeriya baki dayansu su na godiya sosai da irin gudumawar da Gidauniyar Bill da maidakinsa Melinda suke bayarwa ga ayyukan kiwon lafiyar 'yan Najeriya da wasu sassa n ma na tattalin arziki.

Alhaji Aliko Dangote yace akwai bukata ga dukkan masu ruwa da tsaki da su hada hannu domin tabbatar da bunkasa bangaren kiwon lafiya, ta yadda 'yan Najeriya baki daya zasu iya cin moriyar harkokin kiwon lafiyar jama'a a kasar.