Accessibility links

Bill Gates Yana Najeriya a Ci Gaba Da Shirin Yaki Da Cutar Shan Inna

  • Aliyu Imam

Hamshakin dan kasuwan nan Bill Gates.

Hamshakin dan kasuwar nan Bill Gates yana rangadi a Najeriya da nufin wayar da kai kan cutar Polio.

Daya daga cikin manyan masu kudi a doron kasa, kuma shugaban kamfanin kera kayan komputa Bill Gates, ya bayyana farin cikin da samun labarin irin hobbasawar da gwamnatoci daga matakan jihohi da tarayya suke dauka wajen yaki da cutar shan inna a Najeriya.

Hamshakin dan kasuwan ya bayyana haka ne lokacinda ya kai ziyara gidan gwamnatin jihar Lagos, a ci gaba da kokarin da gidauniyarsa take yi na ganin bayan cutar shan inna a Najeriya. Gates ya bayyana fartar ganin da wani dan lokaci kadan za’a shawo kan wannan cuta.

Bill Gates yace ya lura cewa daya daga cikin matsala da yaki da cutar yake fuskanta shine har yanzu ba a baiwa shirin yekuwar da ta kamata wajen ganin iyaye sun fahimci muhimmanci dake tattare da yiwa ‘yayansu rigakafi daga kamuwa da cutar ba.

Da yake maida martani gwamnan jihar Lagos Babaraji Fashola, yace daya daga cikin hanyoyin da yake gani zasu taimaka wajen yaki da cutar shine amfani da wadanda suka kamu da cutar wajen shelar illar cutar shan inna. Gwamnan yace wadannan mutane sun fi kowa sanin abunda zasu gayawa jama’a su shawo kansu.

Haka kuma gwamnan yayi maganar yadda batun addini da al’adu suke taka rawa kan wannan batu.

XS
SM
MD
LG