Gina Gidaje Nesa Da Juna Na Taimakawa ‘Yan Ta’adda

BORNO: Kasuwar Monday

Kwararru a taron kwamitin shugaban Najeriya mai tallafawa Arewa maso Gabas, sun gano cewa gina gidaje nesa da juna a yankunan Borno na samawa ‘yan ta’adda saukin afkawa jama’a.

Kwamitin dake karkashin janar Theophilus Yakubu Danjuma, na ci gaba da tattara bayanai don nasarar sake tsugunnar da mutane a garuruwansu na asali, da kuma cusa akidar tirjiya ga barazanar ‘yan ta’addar a zukatan al’umar yankin.

Masana sun bayar da missalin yadda al’ummar Biu a kudancin Borno suka dakile neman kutsawar ‘yan Boko Haram, da yadda mutanen Azare su ka yi kukan kura suka tinkari ‘yan ta’adda suka kuma samu galaba.

‘Daya daga cikin masu tsara manufofi a kwamitin Farfesa Jibo Ibrahim, ya ce kasancewar yadda aka tarwatsar da ‘yan Boko Haram ya sa suka fara kai hare-haren sari-ka-noke, hakan yasa yanayin gidajen masu nisa da juna ya zamanto tarko ga ‘yan ta’addar kasancewar mutum uku da makamai zasu iya bin gida-gida suna kashe mutane.

Masani Dakta Sani Yakubu Gombe, na fatan kwamitin ya afka aiki bayan an tara bayanai. Biyu bayan korafe-korafe da ya taba samu a baya lokacin da ya gudanar da wani aiki da Majalisar Dinkin Duniya ta tura shi, inda yace akwai korafin jami’an da ke baiwa ‘yan gudun hijira abinci a sansanoni ke neman ‘yan mata kafin su basu abinci.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Gina Gidaje Nesa Da Juna Na Taimakawa ‘Yan Ta’adda - 2'56"