GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali-Magidanci Ya Yiwa Kawar 'Yarshi Ciki-Kashi Na Daya-Agusta,15, 2019

Alheri Grace Abdu

Yau shirin Domin Iyali ya yada zango a garin Misau na jihar Bauchi, inda wani magidanci ya yiwa kawar 'yarshi 'yar shekaru goma sha uku ciki, bayan ya shafe kusan shekaru biyu yana yi mata fyade da tunanin cewa, da yake karamar yarinya ce ba zata yi ciki ba. Tun daga lokacin da asirinshi ya tonu, bayanda wadansu da suka lura yana yawan shiga da yarinyar lungu, suka kwarmatawa yayarta, aka kuma fake shi aka kama shi da ita a daki.

Saurari bayanin mahaifiyar yarinyar.

Your browser doesn’t support HTML5

Tela Ya Yiwa Kawar Yarsa Fyade A Misau-Pt1-10:30"