GREECE: Girkawa Sun Yi Watsi da Kara Tsuke Bakin Aljihun Gwamnati.

Firayim Ministan Girka Alex Tsipras

Ministan kudin Girka Yanis Varoufakis yayi murabus a yau Litinin, kwana daya bayan da Girkawa suka kada kuri’ar rashin amincewa da bukatar masu bin kasar su bashi, na kara takunkumin tsuke bakin aljihun gwamnati, a sakamakon haka zasu kara baiwa kasar tallafin ceto.

Murabus din ministan kudin ya bada mamaki kasancewar ya fada a baya cewar zaiyi murabus ne kawai in har ‘yan kasar suka amince da tsuke bakin alhijun.

Haka kuma Varoufakis ya fada a yau Litinin cewa ya fahimci cewa akwai wasu cikin mambobi a kungiyar kasashe masu amfani kudin Yiro dake da sha’awar ganin an wani ba shi ba a matsayin ministan kudi. Yace fitar sa wata hanya ce da zata taimaka wajen cimma yarjejeniya tsakanin kasar Girka da masu bin ta bashi.

Varoufakis dai ya sha gwabzawa kasashen dake bin kasarshi sau da dama a yan watannin da suka gabata. Dama ‘yan kwanakin da suka wuce, ya zargi kungiyar Tarayyar Turai da cewa kungiyar ta’adda ce, dake kokarin tsorata ‘yan Girka kan su zabi abinda kungiyar ta ke so.