Guguwar Canji Tana da Karfi Yanzu a Najeriya

'Yan rajin neman canji magoya bayan Janaral Buhari

Masani kan harkokin yau da kullum musamman na siyasa yana ganin guguwar canji dake kadawa a Najeriya yanzu tafi ta kowace lokaci karfi

A wata fira da abokin aiki yayi da Dr M.K. Hassan kwararre akan harkokin siyasa da halin zamantakewa yana ganin guguwar canji a Najeriya tana da karfi a wannan karon.

A cikin hukumomin da ake hada baki dasu a yi magudi da can, musamman hukumar zabe da na 'yansanda, da yawa sun gaji. Suna son canji kodayake yanayin aikinsu bai basu damar su nuna a sarari ba. Amma idan lokaci yayi zasu san hikimar aikinsu da zai sa ba zasu yi magudi ba. Domin haka za'a samu canji din.

Kana abubuwan da suka faru a wasu kasashe tun daga kan Ghana a 2007 da Tunisia a 2014 sun sa kasashen su hakura shi yasa babu yadda Najeriya zata yi saidai ita ma ta hakura a wannan karon. Kasar Ivory Coast da taso ta ki canji an ga yadda duniya tayi mata ca, dole ta karbi canji. Da kyar idan hukumomin Najeriya zasu yadda akai ga zubar da jini kafin a samu canjin da mutane ke bukata kamar yadda ta faru a Ivory Coast.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Guguwar Canji Tana da Karfi Yanzu a Najeriya - 2' 00"