Guguwar Trami Ta Afka Kan Japan

Wata mota da ta hantsila sakamakon guguwar ta Trami akan hanyar Uruma, Japan, Sept. 29, 2018

Harkoki sun tsaya cak a Japan sakamkon mahaukaciyar guguwa.

Wata mahaukaciyar guguwa ta ratsa Japan a yau Lahadi, wacce ta janyo aka hana jiragen sama dana kasa aiki ciki har da yankunan Tokyo a lokaci guda kuma jami’ai na gargadin saukar ruwan sama mai karfi gami da iska.

Gonaki da gidaje a Miyazaki, wani tsibiri dake kudancin Kyushu sun makare da ruwa a yayin da guguwar ke ratsa kudu maso yammacin Japan. An bada izinin kwashe dubban mutane a yankuna da masifar ta afkawa, ciki har da birnin Tokushima dake da mutane 250,000 a tsibirin Shikoki a cewar kafar yada kabarai ta NHK.

Kimanin mutane 51 ne suka jikkata a kuduncin na Japan.

An soke tashin jiragen sama a baki dayan Japan, ciki har da Narita da Haneda. Guguwar ta lalata layukan lantarki a kudancin tsibirin Okinawa a jiya Asabar.

Ana tsammanin Trami ta fada birnin Tokyo a daren yau Lahadi, inda zata sauka a arewacin Japan a gobe Litinin.

A watan Yulin da ya gabata ruwan sama mai tsananin karfi yayi sanadiyyar mutuwar mutane 221.