Guterres Ya Yaba Da Yadda Al'amura Ke Daidaituwa A Sudan

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yayin da yake jawabin bude babban taron majalisar na 2019 a karo na 74 a birnin New York

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yaba da ci gaban da ake samu a fagen siyasar Sudan, yayin da gwamnatin wucin gadin da aka kafa take kafa turakun dimokradiyya.

A jiya Juma’a Guterres ya nuna matukar farin cikinsa, yana mai cewa “ranar Juma’a rana ce ta musamman a gare shi, domin ba kasafai ake samun labari mai dadi a taron Majalisar Dikin Duniya ba.”

“Wannan lokacin ne da na fi farin ciki a wannan taron cikin wannan mako. Idan da za a ce shekara daya da ta wuce akwai yiwuwar wannan zama, ban yi tsammanin akwai wanda zai yarda ba. Amma abin farin ciki shi ne ga shi muna bikin kafa sabuwar Sudan.” Inji Guterres.

Sai dai ya ce kafa gwamnatin wucin gadin, mafarin tafiyar ce, ba karshenta ba.

Guterres da kungiyar Tarayyar Afirka, sun yi kira da a dage takunkuman da aka sakawa kasar sannan Amurka ta cire ta daga jerin kasashen da ke marawa ayyukan ta’addanci baya.