Gwamnan Jihar Filato Ya Bayar Da Tabbacin Lashe Zaben Jihar

Buhari a Filato

Gwamnan jahar Filato, Simon Lalong bayyana tabbacinsa na lashe zabe a zaben da za a kammala ranar Asabar mai zuwa.

A ganawarsa da manema labarai a fadar shugaban kasa, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Lalong ya danganta matsalolin tsaro da jahar Filato ke fuskanta cewa siyasa ce kawai.

Sakataren jamiiyyar APC a jahar Filato, Bashir Musa Sati ya ce basu da wata tantama na yin nasara a zaben.

Jibrin Banchir dake zama mai ba gwamnan shawara kan harkokin ma'aikata, ya ce gwamnati ta dauki matakan tsaro a jahar.

A bangare guda kuwa, dan takarar gwamna a karkashin jami’iyyar PDP a jahar Pilato, Jeremiah Useni ya ce sun yi wa jami'ansu garambawul wadanda a baya suka yi amfani dasu, saboda rashin gaskiya da suka nuna a zaben daya gabata.

Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnan Jihar Filato Ya Bayar Da Tabbacin Lashe Zaben Jihar - 3'30"