Gwamnan Jihar Kaduna Ya Ce Ba Ya Sulhu Da 'Yan Bindiga

Ana ci gaba da samun bayanai a game da harin da wasu ‘yan bindiga suka kai jiya Lahadi inda suka kashe kimanin mutum 50 a jihar Kaduna.

A yau litinin gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i, ya bayyana wa al'ummar kauyukan da aka kai harin cewa za a kai jami'an tsaro wuraren don tabbatar da tsaro, kuma ya ce ba zai hau teburin neman sulhu ba da 'yan bindigar dake tada kayar baya ba.

Haka zalika a yau litinin dan majalisar wakilai dake wakiltar karamar hukumar Igabi inda lamarin ya auku, Zayyad Ibrahim ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ya zuwa yanzu dai ba’a tabbatar da hakikanin wadanda suka mutu ba, ya kuma ce ba mamaki adadin ya karu domin masu kai agaji na kan gudanar da aikinsu.

‘Zayyad ya kuma ce 'yan bindigar sun fara da harbe-harbe ne akan jama’a bayan fitowar su daga masallaci, ya kuma kara da cewar wadanda suka raunata an kaisu wasu asibitocin dake yankin.

Shi kuwa Kansila Dayyabu Kerawa, ya ce wannan harin na mai da martini ne akan wani hari da sojojin Najeriya suka kai kan ‘yan bindiga a yankin.