Gwamnan Jihar Katsina Yace Yana Goyon Bayan Sake Fasalin Tsarin Gwamnatin Tarayya.

  • Ladan Ayawa

KATSINA: Gwamnan Katsina Bello Masari

Gwamnanjihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari yace yana goyon bayan sake fasalin Najeriya amma akwai abinda za ayi laakari dasu idan anzo yin hakan

Yayin da ake ta cece kuce game da sake fasalin tsarin Najeriya, Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya shaidawa Sahabo Imam Aliyu ra’ayinsa game da wannan batu, inda yake cewa ya aminta da cewa ba shakka akwai bukatar rage wa gwamnatin tarayya karfi ko kuma ayyuka, to sai dai kuma idan za’ayi sai anyi la’akari da wasu abubuwa.

Yace kowane bangare na da irin nauyin da ya kamata a barshi ya dauka domin kowannensu yana da hanyoyin warware kalubalan dake gabansa.

Gwamna Masari yace ba abinda ya hada gwamnatin tarayya da gina rijiyar burtsatse, ko kuma makarantar Firamare da dai ire-iren wadannan ayyukan.

Sai dai kuma ya nuna cewa amma fa ba kuma za’a rage wa gwamnatin ta tarayya karfi bane ta yadda bata da iko fiye da sauran rukunin gwamnatoci ba.

Ga Sahabo Imam Aliyu da Karin bayani: 2’26

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnan Jihar Katsina yace yana goyon bayan sake fasalin tsarin Gwamnatin Tarayya. 2'26