Gwamnatin Bauchi Ta Fito da Shirin Rage Mutuwar Mata da Jarirai

Mata da jariransu

Gwamnatin jihar Bauchi tare da hadin kan hukumar kiyaye muradun karni ko SDG ta Majalisar Dinkin Duniya ta fito da shirin rage yawan mutuwar mata da jarirai da kuma mata masu ciki.

Gwamnan jihar Bauchi Barrister Muhammad Abdullahi Abubakar ya fayyace abubuwan da shirin ya kunsa a jihar.

Gwamnan yace shirin nada kafofi guda biyar na kiwon lafiya amma cikinsu abu mafi mahimmanci shi ne kula da lafiyar mace da jarirn da aka haifa. Shirin ya kunshi dauke masu biyan kudin magani a asibiti.

Malama Falima Halilu, jami'a mai kula da shirin dorar da muradun karni a jihar Bauchi ta fayyace irin matan da za'a dauka a matsayin nogozoma wadanda zasu dinga taimakawa mata dake kan gwuiwa. Tace zasu dauki matan da suke da dan sani akan kiwon lafiya su taimakawa mata idan hidimar haihuwa ta tashi. Za'a hada matan da masana su kara horas dasu.

Malama Fatima tayi bayanin irin kayan da za'a kawo domin inganta shirin.Kowane asibiti za'a tanadi gadaje, magunguna da motocin daukan marasa lafiya tare da samarda rijiyar bututu.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Bauchi Ta Fito da Shirin Rage Mutuwar Mata da Jarirai - 3' 30"