Gwamnatin Jihar Damagaram a Shirye Take Don Taimakon 'Yan Gudun Hijira

Yan Gudun Hijira a Jihar Damagaram

Ana samun karin 'yan gudun hijira suna shiga jihar Damagaram a kasar Nijar.

Dubban mutane ‘yan gudun hijira na tururuwa zuwa jihar Damagaran a kasar Nijer, a cewar gwamna jihar Damagaran Malam. Kalla Muktari, yace suna samu ‘yan gudun hira da suke shigowa jihar, kumaa shirye suke su taimaka ma duk wadanda ke da bukatar taimako.

Duk dai da cewar wadan da ke shigowar suna zama inda ‘yan uwansu ne kuma har zuwa yanzu babu wani wanda yazo da bukatar neman taimako. Yace gwamnatin shi tashirya don samar da sansanin ‘yan gudun hijira idan bukatar hakan ta samu. Kuma yana kara kira ga al’umar jihar da su cigaba da taimaka ma masu gudun hijirar, kuma su mai da hankali wajen tantance mugu da mutane na kwarai, don kada su kawo matsaloli a cikin jama’a.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnan Damagaram - 5.14"