Gwamnatin Kamaru Ta Sabunta Katin Zama Dan Kasa

Shugaban Kamaru Paul Biya

Bayan ta gano cewa katin zama dan kasa da take anfani dashi bashi da inganci, gwamnatin kasar Kamaru ta fito da wani sabo

Wanda ya jagoranci sabunta katin shi ne Sakataren kasar Kamaru din kuma ya yiwa manema labarai jawabi a birnin Yaounde.

Yace sun yanke shawarar canza katin domin tsohon bashi da inganci. Shi ma babban sifeton 'yansandan kasar yace zasu yi kokari su ga cewa sun ba kowa katinsa.

Gwamnati tana da naurorin da zasu buga kati dubu sittin ko fiye da haka kowace rana.

Mahukuntar kasar sun tabbatar cewa za'a ba kowa katinsa cikin lokaci kankani.

Ga rahoton Awal Garba da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Kamaru Ta Sabunta Katin Zama Dan Kasa - 1' 31"