ZABEN2015: Gwamnatin Najeriya ta Cika Karya - inji Dr Muhammad

Akwatunan zabe

'Yan siyasan Najeriya da mahukunta da gwamnatin kasar sun cika shirga karya

Dr Usman Muhammad yace doka bata cika yin aiki ba a kasar. Wanda yake da kudi da mulki shi ne mai doka a hannu.

Maganar sayen katin zabe ba tun yau gwamnati mai ci yanzu take ta yin wannan nan almundahanan ba. Marigayi Umaru Musa Yar'adua ya fada cewa zaben da ya bashi mulki bai inganta ba. Yace akwai kurakurai da yawa. Duk kurakuran irin su kwace katunan mutane ne ko a je a sauya saka makon zaben karfi da yaji. Akan kuma dauke akwatin zabe a ruga a guje dashi. Akan yi aringizan zabe na wanda bai kamata ba.

To saidai hukumar zabe ta yanzu ta tasan ma yin gyara. Akan yadda mutane suke cigab da sayar da katunan zabensu duk da cewa hukumar zabe tace ba za'a iya yin anfani da katin wani ba a yi zabe, sai yace shi yana ganin mutane basu fahimta ba.

Dan mashin din da INEC ta kawo na tantance masu zabe majalisar dattawa tayi muhawara a kansa da wadanda basa son mashin din domin shugaban hukumar zaben Farfasa Jega yace babu wani tasiri a karbi katin wani a yi zabe. Wannan rashin yiwuwar yasa wasu 'yan majalisar basa son mashin din. Mashin din ba zai yadda da aringizo ba. Da wahala a yi magudi a wannan zaben sabili da dan mashin din..

To amma an fi son a tafi da kati domin a yi aringizon zabe, a canza alkaluman da basu ba ne.

Duk da alkawarin da gwamnatin Najeriya tayi na cewa za'a yi zabe da duniya zata yabawa Dr Usman Muhammad yace an dade ana fadan haka nan amma duk karya ce. Mutane basu yadda da gwamnati ba. Yace gwamnati ma gaba daya idan tace ta nufi kudu to a nemeta a arewa. Gwamnatin Najeriya tayi mugun kaurin suna wajen shata karya. Hukumomin tsaro makaryata ne. Jami'an gwamnati su ma makaryata ne. Sabili da haka da wanene za'a yadda. Kullum 'yan siyasa suka bude baki sai sun fadi karya.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Najeriya ta Cika Karya - inji Dr. Usman Muhammad - 3' 53"