Gwamnatin Najeriya Zata Yiwa Mutane Miliyan 8 Gwajin HIV

Wata karamar yarinya marainiya dake dauke da kwayar cutar HIV

Gwamnatin tarayyar Najeriya tace tana shirin yin wani shirin rigakafi ga mutane tsakanin shekaru goma sha biyar zuwa sama.a kasa baki daya a kokarinta na rage yada cutar kanjamau a kasar
Gwamnatin tarayyar Najeriya tace tana shirin yin wani shirin yiwa mutane tsakanin shekaru goma sha biyar zuwa sama, rigakafi a kasa baki daya a kokarinta na rage yada cutar kanjamau a kasar. Gwamnatin zata yiwa mutane miliyan takwas allurar rigakafi karkashin wannan shirin.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ne ya bayyana haka a wajen wani zama da manyan jami’an gwamnati suke yi inda suka tattauna a kan wannan batun. Shugaban kasar yace, manufar shirin shine a kara yawan mutanen da ake ba magungunan rage karfin cutar HIV da misalin dubu dari shida a kuma samar da maganin kare jarirai da suke ciki daga kamuwa da cutar ga mata dubu dari biyu da ashirin da hudu ga mata masu ciki dake dauke da kwayar cutar.

Shirin zai kuma samar da cibiyoyin kulawa da wadanda suke cikin hatsarin kamuwa da cutar a duk fadin Najeriya. Shugaba Jonathan yace gwamnati zata dauki dukan matakan da ya kamata wajen kare al’ummar kasar daga kamuwa da kwayar cutar HIV da kuma yiwa wadanda suke dauke da cutar jinya domin ceton rayukansu da kuma taimakonsu su bada gudummuwa ga al’umma.

Shugaba Jonathan ya bayyana cewa, duk da kalubalar da ake fuskanta a wannan fannin an sami ci gaba a yaki da cutar kanjamau, aka kuma sami raguwar masu dauke da cutar daga kashi 5.8% a shekara ta dubu biyu da daya zuwa kashi 4.1% a shekara ta dubu biyu da goma, ko da yake akwai sauran aiki a gaba.