Accessibility links

Nigeriya Zata Shiga Jerin Kasashe Dake Fama Da Cutar Suga a 2030


Wani mai ciwon suga yana gwada jini

Masana sun bayyana cewa, kashi 80% na masu fama da ciwon suga a duniya zasu kasance a Najeriya da sauran manyan kasashen duniya a shekara ta 2030.

Masana sun bayyana cewa, kashi 80% na masu fama da ciwon suga a duniya zasu kasance a Najeriya da sauran manyan kasashen duniya a shekara ta 2030.

Masanan sun bayyana haka ne a wajen wani taron likitoci kan kula da Zafin Ciwon Suga wanda kamfanin sarrafa magunguna na Pfizer ya shirya a Abuja. A kan abinda ya sa ciwon ke karuwa masana suka bayyana cewa, yanzu mutane suna rayuwa irin ta al’ummar kaashen yammaci da cin abinci irin nasu, saboda haka ya zama da sauki su rika fama da cututuka irin nasu misali shine wannan ciwon suga da hawan jinni.

Mutum yana kamuwa da ciwon suga ne sa`ad da jiki ya kasa amfani da suga yadda ya kamata, idan jiki baya amfani da suga daidai, to yawancin suga kan karu sosai sannan a kan ce mutum na dauke da ciwon suga

Yanzun haka a duniya, muna da kimanin mutane million 366 da suke dauke da ciwon suga kuma bincike ya nuna cewa a shekara 2030 za a sami mutane wajen million 555 da za su kamu wannan ciwon amma abin tsoron shi ne, kashi 80% na wadanda zasu kamu da ciwon sukar za a same su ne a kaashen masu girma da suka hada da Naijeriya.

Ciwon suga wani mumman ciwo ne wanda idan ba a gane shi da wuri ba, ko kuma idan aka gane amma ba a kula an nemi magani ba yakan shafi dukan bangaren jiki.

Kwararru sun ce hanyar kiyaye ciwon da wuri shi ne gane ciwon da wuri. Saboda haka suka shawarci jama’a su rika zuwa asibiti domin duba lafiyarsu.
XS
SM
MD
LG