Gwamnatin Neja na Binciken Fyade da Aka Yiwa 'Yar Shekaru 14

Ma'azu Babangida Aliyu Gwamnatin jihar Neja

Gwamnatin jihar Neja, taca tana gudanar da bincike akan yarinya ‘yar shekaru 14 da aka yi wa fyade a karamar hukumar Kwantagora a jihar Neja.
Antoni Janar kuma kwamishinan shari’a na jihar, Barrister Abdullahi Bawa Wuse, yace suna gudanar da bincike, amma akwai cikas a binciken.

Barrister Wuse yace “Labarin wannan abun da ya faru yazo wajen mu ranar laraba da yamma, kuma nayi magana da Lauya na dake Kwantagora, kuma ya dauki mataki ya karbi lamarin daga hannun ‘yan sanda.”

Barrister ya jaddada rashin karfin iko, a matsayin wani koma baya, domin bincika lamarin fyaden. “Amma a cikas da muke samu, shine bamu da karfin ikon yin bincike. ‘Yan sanda ne suke da karfin ikon bincike, kuma har yanzu muna kokari mu ga mun samu duka bayannan domin mu cigaba da bincike.”

A yanzu dai, al-umma sun zuba idanu kuma sun kasa kunnuwa domin jin rahoton likitoci zasu bayar akan wannan yarinya.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Binciken Fyade a Jihar Neja - 3:32