Gwamnatin Nijar Ta Fitar da Sabuwar Manufar Hakan Man Fetur a Kasar

Shugaban Nijar Mohamadou Issoufou devant

Kusan duk wadanda suke da hannu a sha'anin hako mai a Nijar kama daga masu filayen da ake hako man da ma'aikatan da ma kasar gaba daya kowa kokawa yake yi saboda illar hakan man.

Gwamnatin kasar bata gane wainar da kamfanin kasar China ke toyawa wajen hakan man. Gwamnati bata san iyakar abun da ake samu ba sai abun da kamfanin ya fada ya samu a rijiyoyin Agadem da matatar Soraz..

Fumukwai Gado ministan man fetur na kasa ya shaida cewa yanzu gwamnati ta fito da wani sabon tsari domin ta mallaki abun dake nata. Yace kasa bata samun komi, masu filaye basa samun komi banda

gidajensu da gonakansu da suka yi hasara. Bugu da kari dabbobinsu na fadawa cikin ramukan da aka tona tare da gurbata muhallansu. Jama'ar wurin da ake hako man ba'a taimaka masu kamar yadda aka yi a yarjejeniyar da aka yi da kamfanin Chinan. An bar mutanen Diffa da Zinder da shan fama.

Yanzu da hukumomin kasar sun fitar da wasu sharudan shifida bututu daga kasar zuwa Kamaru da Togo da Kadunan Najeriya.

Onarebul Sa'adu Dulle na majalisar dokokin kasar yace yanzu majalisar ta kuduri aniyar sa ido kan harkokin kahan man a kasar.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Nijar Ta Fitar da Sabon Tsarin Hakan Man Fetur a Kasar - 3' 11"