Gwamnatin Nijar Ta Karya Farashin Kujerar Zuwa Hajji

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou

Bana gwamnatin Nijar ta rage farashin kujerar zuwa Hajji daga jaka 975 zuwa jaka 900, ragin dake da nasaba da wasu kare karen kudi da mahukumtan Saudiya suka yiwa kowane alhaji dake da niyyar zuwa hajjin 2018

Kodayake an samu dan kari kan kudin da maniyatta suka biya bara hukumar alhazan kasar ta ce karin bai taka kara ya karya ba musamman idan aka yi la'akari da wasu kare-karen da mahukuntan Saudiya suka yi.

Maimakon hakan ma gwamnatin Nijar ta karya farashin tikitin jirgi saboda tabbatar da cewa sabbin matakan da Saudiya ta fitar basu kawo wa alhazan kasar cikas ba.

Alhaji Nuhu Sallau magatakardan hukumar alhazai ta kasa ya ce bara kowane Alhaji ya biya miliyan biyu da jaka dari biyu da wasu 'yan kai. Injishi bana an kara jaka 38 amma abun da Saudiya ta kara ya fi jaka 100. Injishi bara kudin jirgi jaka 975 ne amma bana gwamnatin Nijar ta ce a maida kudin kujerar jirgi jaka 900.

Masu aikin hajji irinsu Abdulaziz Idrisa Jigal shugaban kamfanin Almalase sun yi na'am da matakin da gwamnati ta dauka. Ya ce sun ji dadin rage farashin domin zai taimakawa alhazai matuka musamman tunda a Saudiya an kara wasu kudaden abinci, wurin kwana da dai sauransu.

Bana Nijar nada kujeru dubu goma sha shida, 16,000 da Saudiya ta kayyade mata.

A saurari rahoton Souley Mummuni Barma da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Nijar Ta Karya Farashin Kujerar Zuwa Hajji - 2' 39"