Gwamnatin Siriya Tayi Allah wadai da Kai Hari Kan Sojojinta

Shugaban Siriya Bashar al-Assad

Syria tayi Allah wadai da Harin da Dakarun da Amurka ke jagoranta suka kai a akan wurin da sojojin gwamnati suke, wanda jami’an Syria suka ce yayi sanadiyyar mutuwar mutane da yawa da kuma lalata kayayyaki.

Jami’an Syria sun fada a yau jumma’a cewa harin na jiragen sama da aka kai kusa da Iyakar Syria da Jordan na dakile kokarin Sojojin Syria wajen yakar ISIS.

Rasha wacce take mafi kusanci da Gwamnatin Syria – ta kira wannna hari akan inda sojojin gwamnatin Syria suke a zaman wanda“Bai dace ba.”

A jiya Alhamis ne, Jami’an Amurka suka ce Jirgin dakarun hadakar ya kai hari kan mayakan dake goyan bayan gwamnatin Syria da suka cigaba da sabawa yarjejeniyar ware waje domin horas da mayaka na musamman a matsayin sojojin sakai na Syria.

Mai Magana da yawun rundunar Amurka a gabas ta tsakiya Major Josh Jacques ya fadawa VOA dakarun da ke goyon bayan gwamnatin Syria sun shirya jerin gwanon motocine a Arewa Maso Yammacin barikin Al-Tanf da Tankoki, da kuma Motocin ruguje gini Da kuma Motocin ayki dauke da makamai, gami da Motoocin Sojoji da kuma motocin makanikai, haka kuma sun fara kama wurare domin fara fada da tankokinsu.