Gwamnatin Soji A Sudan Ta Soke Yarjejeniya Da Fararen Hula

Shugabannin riko a kasar Sudan sun ce sun soke yarjejeniyar da suka cimma a baya da masu zanga-zanga fararen hula, biyo bayan harin da dakarun tsaro suka kai jiya Litinin a birnin Khartoum wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 35.

Janar Abdel Fattah al-Burhan, shugaban kwamitin sojin kasar dake riko, a wani jawabi da yayi wanda aka nuna a talabijin yau Tallata, ya sanar da cewa ba tare da bata lokaci ba, za a kafa gwamnatin hadin gwiwa kuma zata shugabanci kasar har zuwa lokacin da za a yi zabe nan da watannin 9. Janar Burhan ya kuma ce za a shirya zaben a karkashin sa idon wakilan yankin da na kasa-da-kasa.

Farmakin da aka kai jiya litinin a wurin da ake zanga-zangar, a wajen ma’aikatar tsaron kasar shi ya kara tabarbarar da tattaunawar da ake yi tsakanin sojoji da ‘yan Alliance for Freedom Change, wato hadakar masu zanga-zanga da jam’iyyun adawa.

Kungiyar Professionals Association ta Sudan, wato babbar kungiyar dake shirya zanga-zangar, ta zargi jami’an tsaro da aikata kisan kiyashi a jiya litinin.