ABUJA: Abubakar Malami ministan shari'a na Najeriya kuma antoni janar
Gwamnatin tarayyar Nigeria tayi alkawarin sa kafan wando daya da duk wani ko wasu da aka samu suna marawa kungiyar 'yan taadda baya.Ministan Shara'a na kasar ne yayi wannan furucin sailin da yake zantawa da Muryar Amurka a Abuja.
WASHINGTON DC —
Wannan sanarwan ta fito daga bakin Ministan Shara’a na kasar, Abubakar Malami, sai’lin da yake zantawa da wakilin muryar Amurka Umar Faruk Musa a Abuja.
Ministan yace tuni gwamnati ta dauki duk matakanshara’ar da suka dace na haramta kungiyar.
Haka kuma ministan yace yanzu haka gwamnatin Nigeria ta fara ganawa da wasu kasashen da take jin cewa wadannan kungiyoyin ‘yan ta’adda nada alaka da su da zummar yi masu bayani