Hadaddiyar Daular Larabawa zata mayar wa Najeriya kudaden sata

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Bisa ga yarjeniyoyin da Najeriya tayi da Haaddiyar Dualar Larabawa yanzu masu satar kudi daga Najeriya suna kaisu kasashen waje, kamar kashinsu ya bushe, basu da sauran wurin buya.

Najeriya da Hadaddiyar Daular Larabawa ko UAE yau Talata suka rabtaba hannu kan wasu yarjejeniyoyi a Abu Dhabi a wani yunkurin karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Muhammad Buhari da Yariman Daular Shaikh Muhammad Bin Zayed Al Nahyam sun kasance wurin sanya hannu akan yarjeniyoyin kasuwanci da cinikakkya da na harkokin shari'a da ma wasu.

Ministar harkokin kudin Najeriya Mrs Kemi Adeosun da takwaranta na Daular Obaid Attayar su ne suka sa hannu akan yarjejeniyar gujewa biyan haraji sau biyu da wasu harkokin yin anfani da kudi.

Shi ma ministan kasuwanci,cinikayya da saka jari na Najeriya Okechukwu Enelamah tare da takwaransa suka rabtaba hannu akan yarjejeniyar habaka kasuwanci da kare muradun juna.

Bayan haka ministocin harkokin shari'a Abubakar Malami na Najeriya da Sultan Bin Saeed Albadi na UAE sun sa hannu akan yarjejeniyar tasa keyar 'yan kasarsu da suka aikata laifi zuwa kasarsu da yin musayar fursinoni da taimakawa juna ta fannin shari'a akan laifuka da suka hada da mayar wa juna kudin sata. Ke nan duk kudaden sata da 'yan Najeriya suka boye a Daular za'a mayar dasu. Ba ma kudi kadai ba duk wata dukiya ko kaddara da aka mallaka da kudin sata za'a mayar da su.

Yayinda yake jawabi lokacin liyafar da aka yi masa shugaba Buhari ya sake jaddada anniyarsa ta cigaba da yaki da cin hanci da rashawa ba sani ba sabo da zummar maido wa Najeriya martabarta cikin kasashen duniya.

Shugaba Buhari ya gargadi kasashen Islama da su goyi bayan yaki da ta'adanci a Najeriya su kuma yi tur da aika aikar 'yan Boko Haram domin su nunawa duniya cewa abun da su keyi bashi da alaka da Musulunci kuma sun sabawa koyaswar Annabi Muhammad (SAW).

Da yake mayar da martani Yarima Zayed Al Nahyan yace dangantaka tsakanin Najeriya da UAE zata samu karfafawa da ziyarar Shugaba Buhari da kuma sa hannun kan yarjeniyoyin da aka yi.