Hankalin Kasashen Duniya Ya Koma Kan Zaben Najeriya 2019

Jakadan Amurka a Najeriya Mr. Stuart Symington

Gwamnatin Amurka tayi kira da a aiwatar da ingataccen Zabe cikin kwanciyar hankali a Najeriya.

Da yake jawabi a wani taron tabbatar da an gudanar da Zaben cikin kwanciyar hankali, tare da kaucewa rashin hankali, Jakadan Amurka a Najeriya, Ambasada Stuart Symington ya ce duk duniya babu inda za ai Zabe mai mahimmancin da ya kai na Najeriya.

Jakadan na Amurka yace suna fatan ganin an shirya babban zaben cikin gaskiya, adalchi, 'yanci da sanin ya kamata.

Shima cikin jawabinsa, Daraktan wata kungiyar kasa-da-kasa dake sa ido kan harkokin zabe Dr. Darius Redcliff ya yabawa hukumomin tsaro sannan yayi fatan zasu dage wajen yin Adalchi batare da nuna son rai ba.

A baya bayannan dai Amurka na kara nuna damuwa, da sha'awa dangane daftarin demokaradiyyar Najeriya, al'amarin da wani kwararre Alhaji Baba Ba'abba Dan masanin Fika, ke cewa bai rasa nasaba da yadda Amurkan ke son ganin dorewar tsarin na demokaradiyya.

Baba Ba'abba yace in tsarin demokaradiyyar Najeriyar ya kan kama sosai, to itama zata ci moriyar hakan, duba da irin alakar kasuwanci dake tsakanin kasashen biyu.

Wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka Hassan Maina Kaina, ya hada muna wannan rahoto.

Your browser doesn’t support HTML5

Hankalin Kasashen Duniya Ya Koma Kan Zaben Najeriya 2019 2'10"