An Gaza Gano Wadanda Suka Nemi Hallaka Tsohon Sakataren Sarkin Kano

hotunan Bukukuwan hawan nassarawa da aka gudanar a kano

Kimanin mako guda bayan wasu ‘yan bindiga sun yi yunkurin kashe tsohon sakataren sarkin Kano Alhaji Isa Sanusi Bayero,ya zuwa yanzu rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta ce ba ta kai ga kama wadanda suka kai harin ba, amma ta ce jami’anta na ci gaba da gudanar da bincke.

Alhaji Isa Sanusi Bayero wanda aka fi sani da Isa Pilot, ya kwashe shekaru da dama yana aikin tukin jirgin sama gabanin ya zama sakataren sarkin Kano a zamanin marigayi Alhaji Ado Bayero kafin daga bisani ya yi murabus wani lokaci cikin wannan shekara.

Da almurun asabar din makon jiya ne, wasu mutane su biyar dauke da bindigogi suka je gidan Alhaji Isa Sanusi Bayero dake Unguwar Sharada Phase one a nan Kano da nufin kawar da rayuwar sa, kamar yadda ya shaidawa Muryar Amurka.

Yanzu haka rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano tace tana gudanar da bincike da nufin zakulo wadanda ke da hannu ga wannan yunkuri na kisan gilla, kamar yadda kakakin rundunar SP Magaji Musa Majiya ya tabbatar.

Saurari Rahoton Mahmud Ibrahim Kwari

Your browser doesn’t support HTML5

Yunkurin kashe tsohon sakataren sarkin Kano--4:00"