Har Yanzu Ana Fuskantar Mawuyacin Halin Rayuwa a Najeriya

Yayin da ake ci gaba da neman hanyar magance annobar Coronavirus, yanzu matsalar dake addabar jama’a musamman talaka ita ce mawuyacin halin rayuwa, da suka hada da rashin kudi da kuma tsadar rayuwa.

Kawo yanzu gwamnatin tarayyar Najeriya da kuma jihohi na ikirarin kashe dubban Miliyoyin Naira wajen tallafawa masu karamin karfi, domin rage radadin wahalar rayuwa da ake fama da ita sakamakon annobar Covid-19 da aka fi sani da coronavirus.

Ahmad Tukur Jada, daya daga cikin shugabanin kungiyoyin kananan manoma a Najeriya, ya bayyana wa sashen Hausa irin kalubalen da talakawa ke fuskanta a wannan lokaci na annoba, wanda ya hada da tsadar rayuwa. Game da batun tallafin corona kuwa ya ce babu abin da suka gani.

Sai dai yayin da talakawa ke kokawa, tuni wasu wakilai da kuma kungiyoyi suka fara neman hanyar tallafawa, domin ragewa al’umma wahalar da suke ciki.

Dan Majalisar Dokokin jihar Taraba, Bashir Muhammad Bape, ya fadawa Muryar Amurka cewa a mazabarsa ta Nguroje, sun sayi Babura guda 60 da injinan markade da kuma Kekunan dinki suka rabawa al’umma domin su sami hanyar gudanar da rayuwa.

Ya zuwa yanzu dai, an bude wasu kasuwanni a jihar Taraba sai dai ana kokawa kan yadda wasu kayayyakin more rayuwa irin su Hatsi da masu karamin karfe matukar bukata na kara yin tashin gwauron zabi.

Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Har Yanzu Ana Fuskantar Mawuyacin Halin Rayuwa a Najeriya - 3'30"