Har Yanzu Jami'an Tsaro Na Tare Motoci Suna Karban Na Goro

Jami'an tsaro na karban kudi hannun masu tuka ababen hawa alatilas

Kodayake babba sifeton 'yansandan Najeriya ya bada odar kada 'yansanda su cigaba da tare hanyoyin Najeriya amma har yanzu jami'an tsaro na cigaba da tare hanyoyi a jihohin Adamawa da Taraba inda suke tilastawa masu ababen hawa basu kudaden da suka bukacesu su biya

Yanzu haka dai da alamun har yanzu wasu ma’aikatan tsaro da suka hada da ‘yansanda basu bi umarnin cire shingayen bincike da babban sufeton ’yansandan Najeriya Ibrahim Idris ya bada a makon jiya.

Da farko dai 'yan Najeriya da yawa sun yi maraba da wannan mataki domin galibi shingayen tamkar hanyar samun damar karbar na goro ne daga matafiya da kuma masu jigilar kayayyaki da ‘yansanda ke yi.

To sai dai kuma da alamun da sauran rina a kaba domin duk da wannan umarnin har yanzu ana cigaba da samun jami’an tsaro akan hanya suna karban na goro, inda a wasu lokutan ma sukan maida ranakun kasuwanni tamkar ranar karbar shara inda sukan tsaya kan haya don karbar na goro daga matafiya.

Alal misali a jihohin Taraba da Adamawa, irin wadannan jami’an tsaron, musamman yan sanda da sojoji, kan tsaya ne akan babbar hanya, kuma ba tare da fargaba ba,sukan bayyana abun da suke bukata, batun da direbobi ke cewa ya wuce mizani.

Wani lokaci ma ba direbobi kawai ake tatsa ba, harda fasinjoji.

Sai dai kuma a kullum jami’an tsaron kan nemi musanta zargin karbar na goron da ake yi, kamar yadda kakakin rundunan yan sandan jihar Taraba David Misal ya musanta a zantawar da yayi da wakilinmu Ibrahim Abdulaziz.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Har Yanzu Jami'an Tsaro Na Tare Motoci Suna Karban Na Goro - 3' 33"